1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Boko Haram an bar baya da kura

July 30, 2019

Rikicin kungiyar Boko Haram shekaru bayan kisan Mohammad Yusuf a Najeriya ya haifar da rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali a ciki da wajen kasar, tare da yada akidar kungiyar a wasu kasashe makwaftan Najeriya.

https://p.dw.com/p/3N1Id
Nigeria Damasak Soldat Boko Haram Wandbild
Hoto: Reuters/J. Penney

Kungiyar Boko Haram ta shafe tsawon shekaru 10 tana kai hare-haren ta'addanci a Najeriya ciki har a fadar gwamnatin tarayyar dake a Abuja. Rikicin da ya kara ta'azzara al'amurra na rayuwa da walwala dan Adam a yankin Arewa maso gabashin Najeriya, ya salwantar da rayukan jama'a dubu 100, sai dai a kokarin da gwamnatin Najeriya ke yi don yakar 'yan kungiyar, har yanzu akwai sauran jan aiki a gaba wajen kawo karshen rikicin.

Wannan lamarin ya sa kara saka sahkku a zukatan jama'a da ke yiwa yaki da kungiyar Boko Haram kallon wankin hula na son kai gwamnatin ta tarayyar Najeriya dare.

A fira da DW Hausa kakakin fadar gwamnatin Najeriya Garba Shehu ya bayyana cewa duk da hare-haren da ake samu na kungiyar sojojin kasar da ke bakin daga sun kusa kawo karshen tarzomar, a yayin da gefe daya kungiyoyin kare hakin bani Adama irinsu Amnesty International ke cewa jami'an tsaro na cin zarafin jama'a da sunan yaki da kungiyar Boko Haram.