Boko Haram na ci gaba da kai farmaki | Labarai | DW | 06.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Boko Haram na ci gaba da kai farmaki

A Najeriya kungiyar Boko Haram da ke gwagwarmaya da makamai ta yanka wasu mutane bakwai a garin Ngamdu da ke jihar Borno a yankin arewa maso gabashin kasar.

Shaidun gani da ido Musa Abor da kuma wani jami'in gwamnatin jihar ta Borno da ya nemi a sakaye sunansa sun shaidawa manema labarai cewa sun fito da safe sunga gawarwakin mutanen bakwai an yi musu yankan rago. Shima wani jami'in tsaro a yankin da ya nemi a boye sunansa ya ce makwanni biyun da suka gabata sunyi arangama da 'yan Boko Haram din a garin Ngamdu inda suka hallaka kimanin 15 daga cikinsu wanda ya ce hakan ya sanya sun sha alwashin daukar fansa a kan al'ummar garin.

Ana dai kallon kisan wadannan mutane bakwai da kungiyar ta Boko Haram ta yi a matsayin ramuwar gayya ga kashesu da jami'an tsaron Najeriyar suke yi a 'yan kwanakin nan. Hare-haren kungiyar ta Boko Haram dai ya hallaka sama da mutane 10,000 tun bayan da aka fara shi a shekara ta 2009 kawo yanzu.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Suleiman Babayo