Bishop ya yi murabus a Najeriya | Labarai | DW | 19.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bishop ya yi murabus a Najeriya

Fadar Vatikan ta sanar da murabus na wani Bishop na darikar Katholika a jihar Anambara da ke yankin kudancin Najeriya sakamakon rashin iya warware takaddamar da ta biyo nadinsa a matsayin na Bishop.

Vatikan Papst hält Weihnachtsansprache (Reuters/M. Rossi)

Jagoran darikar Katholika na duniya, Paparoma Francis

Fadar Vatikan ta sanar da murabus din wani Bishop na darikar Katholika a jihar Anambara da ke yankin kudancin Najeriya sakamakon rashin iya warware takaddamar da ta biyo nadinsa a matsayin na Bishop. Shi dai Bishop Peter Ebere Okpaleke, ya fuskanci turjiya daga al'umar yankin Igbo ne, shekaru shida bayan nadinsa da paparoma Benedict da ya gabata ya yi.

Al'umar yankin na Anambara, sun bijire wa nadin Bishop Eberen ne saboda kasancewar shi mutumin jihar Imo ba kuma dan jihar ta su ba. Da fari dai Paparoma Francis ya yi kokarin kare nadin nasa, tare da kokarin sulhunta manyan limaman Katholikan yankin cikin watan Yunin bara, sai dai abin ya gaza samun nasara.