Birtaniya ta bukaci taimakon EU | Labarai | DW | 17.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Birtaniya ta bukaci taimakon EU

Firaministar Birtaniya Theresa May, ta bukaci hadin kan kungiyar Tarayyar Turai EU ta fuskar mu'amalar tsaro bayan ta fice daga cikin kungiyar.

Firaministar Birtaniya Theresa May, ta bukaci hadin kan kungiyar Tarayyar Turai EU ta fuskar mu'amalar tsaro bayan ta fice daga cikin kungiyar. Yayin jawabin da ta gabatar lokacin taron harkokin tsaro a birnin Munich, madam May ta ce rayuwar jama'a na cikin hadari.

Ta amince cewa babu wata kasa ta daban da ta fi Birtaniyar kyawun alaka da kungiyar ta EU, a saboda haka ne take cewa babu dalilin da zai hana su cimma wannan bukata. Firaministar ta Birtaniya, ta kuma ce ba za su bata lokaci wajen cimma batun na tsaro ba, tana mai gargadin kasashen Turai da su guji sanya siyasa cikin matsalolin da suka shafi kokari na yaki da ta'addanci.