Theresa May na fafutukar ceto Brexit
January 17, 2019Talla
Firaministar Birtaniya Theresa May ta fara tattaunawa da sauran shugabannin jam'iyyun siyasar kasar a wani yunkuri na lalubo mataki na gaba da za si dauka kan ficewar Birtaniya daga Tarayyar Turai.
Wannan dai na zuwa ne bayan da Mrs. May ta tsallake rijiya da baya kan kuri'ar yankan kaunar da aka kada jiya Laraba. Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da majalisar ta yi watsi da daftarin da firamistar ta gabatar kan ficewar kasar daga kungiyar ta EU.
Nan da ranar Litinin mai zuwa ne Firaministar ta Birtaniya za ta gabatar da tsare-tsarenta kan inda gwamnatinta ta dosa kan batun na barin EU din.