Birtaniya da NATO na nazarin tsaron yankin Arctic
January 12, 2026
Gwamnatin Birtaniya ta ce tana tattaunawa da kungiyar kawancen tsaro ta NATO kan yadda za a kara inganta tsaro a yankin Arctic, domin tunkarar barazanar Rasha da China.
Ministar sufuri ta Birtaniya, Heidi Alexander, ta ce tattaunawar mataki ne da suka sabda daukai na yau da kullum, ba wai martani ba ne ga kalaman Shugaban Amurka Donald Trump kan barazanar mallakar Greenland da ke a yankin Arctic.
A ranar Juma'a Trump ya ce yana son kulla yarjejeniya domin mallakar Greenland, wani yanki mai cin gashin kansa na kasar Denmark, yana mai cewa hakan zai hana Rasha ko China samun iko da yankin. Ya kuma bayar da tabbacin Amurka za ta dauki mataki kan Greenlandko da kuwa ta fuskanci adawa mai zafi kan yunkurin.
Greenland na da al'umma kusan 57,000, kuma Denmark ce ke kula da tsaronta, duk da cewa Amurka na da sansanin soji a tsibirin. Firaministar Denmark ta gargadi cewa duk wani yunurin kwace yankin zai iya zama barazana ga kungiyar NATO.