Bikin sake bude cocin Frauenkirche a birnin Dresden na jihar Saxony | Labarai | DW | 30.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bikin sake bude cocin Frauenkirche a birnin Dresden na jihar Saxony

Shekaru 60 bayan an yi masa raga-raga a yau aka yi bikin sake bude cocin Frauenkirche na birnin Dresden bayan aikin sake gina shi. A cikin wa´azin da yayi bishop din jihar Saxony Jochen Bohl ya ce cocin na matsayin wata alama ta sasantawa da kuma wanzar da zaman lafiya. Shi kuma a nasa bangaren shugaban tarayyar Jamus Horst Köhler ya kwatanta sake gina cocin da cewa wata kyakkyawar alama ce ta dorewar sake hade Jamus da kuma yin sulhun tsakanin kasar da sauran al´umomin duniya baki daya. Kimanin mutane dubu 60 ne suka halarci bikin sake bude cocin. Daga cikin manyan baki kimanin dubu 1 da 700 da aka gayyata har da shugaban gwamnatin Jamus mai barin gado Gerhard Schröder da kuma wadda zata gaje shi wato Angeler Merkel.