1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

DW ta cika shekaru 65 da kafuwa

Christoph Strack SB
April 12, 2021

Sannu a hankali cikin shekarun da aka kwashe ana fadada harsuna da tashar ke amfani da su, kuma tashar ta fara daga birnin Kolon na Jamus kafin sauya matsuguni zuwa birnin Bonn.

https://p.dw.com/p/2z30C
Konrad Adenauer und DW-Redakteur Hans Wendt Archivbild 1963
Tsohon shugaban gwamnatin Jamus Konrad Adenauer a hira da editan DW Hans Wendt a shekarar 1963Hoto: DW

A ranar Talata a birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus aka yi bikin cikar tashar DW shekaru 65 inda mahalarta taron suka hada da shugabar gwamnati Angela Merkel da sauran jiga-jigan 'yan siyasa. Tashar ta fara watsa shirye-shiyenta ne da muryar tsohon shugaban kasar Jamus, Theodor Heuss, da aka watsa ranar 3 ga watan Mayu na shekarar 1953. Tashar DW ta fara wannan gagarumin aiki ne ta gajeran zangon rediyo daga birnin Kolon inda tashar ke isa bangarorin duniya farko cikin harshen Jamusanci kadai, inda aka fara kara harsunan kasashen ketere daga farkon shekarar 1954. A shekarar 1992 aka fara tashar talabijin ta Jamusanci daga bisani lamura suka karfafa. Shugaban tashar DW a yanzu, Peter Limbourg, ya nuna yadda lamura suka sauya a tsawon shekaru 65 da suka gabata:

"Ina tsammanin akwai lokacin da muka kasance muryar Jamusawa da ke kasashen ketere yanzu muna yada bayanai ga mutanen da ke sassan duniya. Haka ya nuna mun tsaya ga 'yancin 'yan jarida da 'yancin fadin albarkacin baki. Babban abin da yake da muhimmanci shi ne kai bayanai ga mutanen da ba za su iya samun wadannan bayanai a kasashensu ba."

Deutsche Welle, Bonn
Hedikwatar Deutsche Welle a birnin BonnHoto: M. Becker/dpa/picture alliance

Sannan shugaban ya yi nuni da kalubalen da ake fuskanta bisa tabbatar da tsare-tsaren tashar, ga kuma kafofin sada zumunta ga tashoshin da DW ke hulda da su. Tashar kan gabatar da labarai da bin diddigin gami da saka tunani ga mutane bisa abubuwan da suke faruwa.

 

Albarkacin bikin cika shekaru 65 majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ta girmama tashar. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta kasance bakuwa ta musamman da jawabi bisa hanyar gano labarai na kage, yayin da minista a gwamnatin Monika Grütters ke jaroganci zaman muhawara. Tashar ta DW kan bayar da lambobin yabo ga mutanen suka tsaya kan tabbatar da 'yancin fadin albarkacin baki, kuma shugaban tashar Peter Limbourg ya yi karin haske:

Deutschland Deutsche Welle DW Gebäude
Hedikwatar Deutsche Welle a birnin BerlinHoto: picture-alliance/dpa/ZB

"Haka, ina tunani ya dace a dubi wannan lambar yabo kan yadda haka zai taimaki  mutanen da nuna yanayin da suke ciki. Yana da matukar muhimmanci ga suke rayuwa wajen da babu 'yancin bakin albarkacin baki a nuna musu cewa duniya tana kallon abin da ke faruwa."

Yanzu haka ana yada labarai cikin harsuna hudu a tashar talabijin ta DW, sannan harsuna 30 a radiyo da kafar Internet gami da karin bayanai ta kafofin sada zumunta na zamani. Kana akwai bangarren horas da 'yan jarida da ke aiki tun shekarar 1965, inda dubban 'yan jarida suka samu horo. Yayin da tashar DW ke cika shekaru 65 an sake samun makamancin yanayin siyasa na wancan lokaci, akawai maganar sake komawa yakin cacar baka da tauye 'yancin fadin albarkacin baki. A biranen Bonn da Berlin DW tana da ma'aikata kimanin 3,400 daga kasashe fiye da 60 na duniya. Tashar DW ta shahara a sako da lungu na duniya.