Bikin cika shekaru 100 da hade yankunan Najeriya | Siyasa | DW | 31.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bikin cika shekaru 100 da hade yankunan Najeriya

A tsawon wadannan shekaru Najeriya ta ga sauye-sauye masu tarin yawa sai dai har yanzu 'yan kasar na korafin rashin samun wani ci-gaba na a zo a gani.

A yayin da Najeriya ke bikin cika shekaru 100 da hade kudanci da arewacin kasar da turawan mulkin mallaka suka yi a garin Zungeru na jihar Niger, har yanzu al'umomin yankin na ganin babu wani abin a zo a gani da suka amfana daga gwamnatin tarayya balantana ta jiha.

A Zungeru a kan wani tsauni akwai wata makabartar turawa 'yan mulkin mallaka da suka rasu a lokacin da gwamna Lugga ya kafa hedkwatar Najeriya a Zungeru ko Dungurun kamar yadda ake kiran garin a da.

Kuma wannan gari na kan hanyar zuwa Tegina ne, bayan an fito daga Minna, kuma garin na Zungeru yana gaban kogin Kaduna ne, akwai kuma tashar jirgin kasa.

Rashin ci-gaba mai gamsarwa

To sai dai kuma bayan wannan alama na 'yan mulkin mallakan babu wani abun a zo a gani da ke nuna cewar wannan gari ya taba zama hedkwatar Najeriya. Hasali ma a nan ne gwamna Lugga ya hade arewaci da kudancin Najeriya.

Malam Ahmed Hameedu mai sharhi ne a kan harkokin yau da kullum kuma wani wanda ya taso a garin na Zungeru ya kuma koka kamar haka:

Sai dai a bangarenta gwamnati ta ce duk da cewar babu wani abin a zo a gani da gwamnatin tarayya ta tsinana masu shekara da shekaru bayan samun 'yancin kai, karamar hukumar Wushishi da garin na Zungeru ke karkashinta, tana gudanar da ayyuka na samar da sana'oi da kananan ma'aikatu domin ci-gaban yankin kamar yadda shugaban karamar hukumar ta Wushishi Alhaji Ahmed Abubakar ya sheda.

Kawo yanzu dai makudan kudade ne aka ce gwamnatin tarayya ta ware domin gudanar da wannan biki, kudaden da wasu ma ke ganin kamata ya yi a yi amfani da su wajen gina al'umma a maimakon sharholiya, kamar yadda Malam Danladi Aboki ke cewa.

Madatsar ruwa don raya kasa

DW_Nigeria_Integration2

Shugaba Goodluck Jonathan

A kwanan baya ne dai shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya kaddamar da aikin gina wata madatsar ruwa a Zungerun, aikin da aka fara shi tun a zamanin gwamnatin Alhaji Shehu Shagari, kuma binciken da wakilinmu Babangida Jibril ya gudanar ya nuna cewar aikin walau dai ya sake tsayawa ko kuma yana tafiyar hawainiya. Abinda kuma yake da nasaba da biyan diyyar gonakin jama'ar da wannan aiki zai shafa da kuma samar da sabbin matsugunai, kamar yadda shugaban karamar hukumar ya nuna.

A sakonsa ga 'yan Najeriya domin wannan biki dai, shugaba Jonathan ya yi kira ga 'yan Najeriya da su manta da banbance-banbancen dake tsakaninsu na addini da harshe ko yanki domin tsallakewa ga tudun mun tsira da nufin ci-gaban kasa baki daya.

Mawallafi: Babangida Jibril
Edita: Mohammad Nasiru Awal

Sauti da bidiyo akan labarin