1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Biden ya caccaki Donald Trump

March 8, 2024

Shugaba Joe Biden ya yi kakkausar suka ga abokin hamayarsa Donald Trump yana mai zarginsa da mika wuya ga shugaban Rasha Vladimin Putin, abin da ya siffanta da tozarci ga siyasar Amurka.

https://p.dw.com/p/4dIHj
Biden ya yi kakkausar suka ga Trump
Biden ya yi kakkausar suka ga TrumpHoto: SHAWN THEW/REUTERS

A yayin jawabinsa na shekara ga majalisar dokokin Amurka, shugaba Joe Biden ya ce wannan abin kunya bai taba faruwa ba a Amurka tun lokacin shugaban kasar na farko Abraham Lincon sai a lokacin Donald Trump wanda ya zarga da jefa kasar cikin koma baya mafi muni a tsawon tarihi. 

A daya gefe kuma mista Biden ya ce ya bai wa sojojin kasar umurnin samar da hanyar shigar wa al'ummar zirin Gaza da kayan abinci sannan kuma ya bukaci tsagaita wuta take yanke na makonni shida. 

Karin bayani: Biden da Trump sun yi fintinkau a "Super Tuesday"

Jawabin na Biden mai shekaru 81 a duniya na shirin bude hamayya mai zafi tsakaninsa da Donald Trump mai shekaru 77 wanda ya sha alwashin mayar masa da raddi ta hanyar muhawara da ya bukaci su yi kafin a je zaben shugaban kasa na watan Nuwamba.