Bene ya rufta kan jama′a a Indiya | Labarai | DW | 31.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bene ya rufta kan jama'a a Indiya

Masu aikin ceto a Mumbai babban birnin kasar Indiya, na can suna kokarin zakulo wasu mutane 40, da wani bene ya rufta a kansu inda hukumomin kasar suka ce an sami asarar rayuka.

Benen mai hawa hudu da ke yankin Bhendi Bazaar mai cunkoson jama'a, ya fadi kan mutanen ne da jijjifin safiyar yau Alhamis, sakamakon ruwan sama da aka yi ta shararawa, da kuma ya halaka rayuka akalla 10. Ya zuwa yanzu dai an tabbatar da ceto mutane hudu daga baraguzan benen, da ke dauke da wasu iyalai akalla tara wadanda ke da gidajensu ciki. Matsalar rushewar gine-gine dai ba sabuwar aba bace a kasar Indiya a 'yan shekarun nan, musamman a lokutan da ake samun ruwan sama mai karfi.