1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

"Bautar da 'yan Afirka da aka yi babban laifi ne" Mahama

Abdul-raheem Hassan
March 25, 2026

Majalisar Dinkin Duniya za ta kada kuri'a kan kudirin da ya ayyana cinikin bayi da aka yi wa kasashen Afirka a matsayin "laifi mafi girma ga bil'adama," Masu kare hakkin bil'adama na maraba da matakin a matsayin waraka.

https://p.dw.com/p/5B6EG
Shugaban kasar Ghana,  John Mahama a zauren MDD
Shugaban kasar Ghana, John Mahama a zauren MDDHoto: Jeenah Moon/REUTERS

Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama daya daga cikin masu goyon bayan kungiyar tarayyar Afirka ta AU kan neman a biya Afirka diyyar bautar da aka yi musu, ya ziyarci hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya don yada wannan da'awa.

Kudurin, kamar yadda ya shaida wa Majalisar Dinkin Duniya a ranar Talata, "ya ba wa Afirka dama a matsayin al'ummar duniya baki daya mu ba da shaida kan halin da ake ciki na sama da mutane miliyan 12.5 wadanda aka sace fatansu da mafarki da makomarsu tsawon shekaru 400."

Da yake kiranta da "kariya daga mantuwa," Mahama ya dauki niyyar yunkurin siyasa na baya-bayan nan a Amurka na haramta littatafai kan wannan batu domin "hana koyar da dalibai gaskiyar abin da ya faru a kan bauta da wariyar launin fata."