1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dinkin Duniya: Hana cinikin bayi

Abdourahamane Hassane AMA
August 23, 2021

Kasar Togo na daya daga cikin kasashen da aka rika tattara bayi daga kasashen Afirka kafin safarar su zuwa kasashen Amirka da Birtaniya da Portugal da kasashen Turai.

https://p.dw.com/p/3zNl9
Sklaverei Sklaven in Afrika
Hoto: Getty Images

Ana tuna wannan rana ce domin tunawa da irin boren da ya fara barkewa a daren 22 zuwa 23 na Augusta a shekara ta 1791 a kasar Saint Dominik wacce a yau ake kiranta da suna Haiti inda jama'a suka tayar da balli na kin ci gaba da amincewa da cinikin bayin, abinda ake ganin ya taka muhimmiyar rawa wajen soke cinikin bayin, kafin daga baya majalisar dokokin Birtaniya ta zartas da dokar haramta cinikin bayin a shekara ta 1807 sannan bayan shekara daya kacal Amirka da wasu sauran kasashen duniya suka amince da dokar a 1808. Bayan haka ne kimani jiragen ruwa na Amirka dubu 7750 suka kwaso bakar fata kusan miliyan biyu da rabi galibi 'yan kasashen Afirka bayi domin mayar da su a Kuba wasu kuma suka ci gaba da zama can har abadan aba da.

An dai fara cinikin bayi ne tun a karni na 15 zuwa nahiyar Turai, Amma  bayan da aka gano Amirka a lokacin aka fara safarar bakar fata zuwa can domin yin aiki a cikin gonaki. Kasar Togo ta kasance daya daga cikin kasashen Afirka da ke bakin tekun inda ake da gidajen tattara bayin kafin a yi safararsu daga nan zuwa Amirka da sauran kasashe. Gidan bayin na da nisan kilomita 30 daga Lome babban birnin Togon.

Karin Bayani: Ranar tunawa da cinikin bayi ta duniya

Gaskin Kpoti Mensah shi ne ke yi wa maziyarta jagora a gidan ajiye bayin na WOOD ya ce "Tarihin wannan gida ajiye bayi  ya fara ne daga lokacin da aka kawo karshen cinikin bayin. Wasu daga cikin masu sayar da bayin da suka bujerewa dokokin cinikin na wadanda kan zuwa nan a boye su yi cinikin bayin."

An gana wa bakar fata azaba a matsayin bayi

Sklaverei
Hoto: Getty Images/Hulton Archive

Gidan na bayi Wood tsakaninsa da bakin gabar teku bai wuce mita biyar ba, kuma an rika dai samun cunkoson bayi wanda samun wurin tsayuwa ma kan yi wuya ga bayin a cewar Gaskin Kpoti Mensah "A cikin dan daki bayi na tsugune wasu gwance ko zaune saboda ba za su iya yin tsaye ba domin dakin dan kurkutu ne bashi da tsawon da za ka iya mikewa tsaye."

Karin Bayani: Sengbe Pieh Bajinta lokacin cinikin bayi

Sau tari bayin kan yi rairahe domin domin fita ko shiga daga dakin saboda karancinsa, akan mika musu abinci ta taga ko a kira wasu daga cikinsu. Akasari mata wadanda da ke cikin, a cikin dare ake yi musu fayde, kana masu cinikin bayan kan kawo su ne daga wurare dabam-dabam a cewar Assiakolé Mensa Edoé babban jami'in da ke kula da gidan ajiye bayin "Suna kawo bayin daga can arewacin Togo a nan, ko da shike a baya ba Togo ake cewa ba. Idan sun zo da rairahe a kan shigar da su dakin wasu a kwance wasu tsugunu har lokacin da za a fitar da su zuwa waje."

An kiyesta cewar mutane miliyan goma zuwa 20 bakar fata daga nahiyar Afirka aka tafi da su zuwa Amirka a matsayin bayi inda aka sayar da su wanda a yau jikokinsu da tattaba kunne suka kasance bakar fatar Amirka.