Birtaniya: Taron yaki da matsalar cinikin bayi | Labarai | DW | 21.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Birtaniya: Taron yaki da matsalar cinikin bayi

Masu shigar da kara a madadin gwamnati daga kasashen duniya sun shiga zaman wani taro da aka tsara da zummar yaki da matsalar cinikin bayi da ta kunno kai a wannan karni, a birnin London.

Taron na kwanaki uku wanda kuma shi ne irinsa na farko ya samu mahalarta daga sassa daban ciki har da wakilai daga kasashen Najeriya da Sudan da kuma Albaniya. An tsara samar da hanyoyi da za a bi don hukunta wadanda aka kama da laifin safarar mutane ko bautar da jama'a.

An shirya duba hanyar kwace kudi dama kadarori daga gungun masu sana'ar safarar mutane da aka kiyasta cewa suna samun kudin shiga da ya kai dalar Amirka biliyan dari da hamsin a duk shekara.

Bincike kungiyoyi na masu rajin kare hakkin bil'adama na cewa akwai mutane fiye da miliyan arba'in da ake bautarwa a matsayin bayi a sassan duniya. A bara an gano a kasar Libiya yadda ake cinikin bakaken fata ciki har da 'yan Najeriya da aka yi ta siyarwa kan dala dari hudu lamarin da ya janyo suka daga sassan duniya.