An haifi John Dramini Mahama a cikin shekarar 1958. Mahama masanin tarihi, kana kwararre a fuskar sadarwa sannan mutum ne mai son rubuce-rubuce.
A shekarar 2012 ne ya hau kujerar shugaban kasar Ghana bayan da shugaban kasar na wancan lokacin John Atta Mills ya rasu. Gabannin zamansa shugaban kasa, Mahama ya rike mukamin dan majalisa dokoki da minista da kuma mataimakin shugaban kasa.