1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bashi ya yi wa Najeriya daurin gwarmai

January 5, 2023

A Najeriya, gwamnatin shugaba Buhari, za ta bar wa kasar bashin Naira Triliyan 77, a daidai lokacin da ya rage mata watanni shida ta sauka kan karagar mulki.

https://p.dw.com/p/4LncX
Nigeria | Verleihung der Nationalen Ehrenauszeichnung
Hoto: Ubale Musa/DW

Tun ba'a kai ga ko'ina ba dai mahukuntan tarrayar Najeriyar suka dau 'yar bashi da nufin cika alkawarin da ke tsakaninsu da miliyoyi na masu zabe na kasar.

To sai dai kuma suna shirin kare wa'adi na shekaru takwas bisa mulki tare da kafa tarihin kwasar bashin dake zaman mafi yawa cikin kasar.

A karon farko dai gwamnatin ta ce tana shirin barwa kasar bashin da ya kai Naira triliyan 77 ya zuwa karshen Mayun da ke zaman wa'adi na gwamnatin APC mai mulki.

Karin bayani: Najeriya: Gibi a tattalin arzikin kasar

Daukaci na manya na tituna da gadoji da shi kansa kokari na mai da layin dogo na zamani cikin kasar dai na tafiya ne bisa doron bashin ciki dama wajen kasar.

Takardar kudi na Naira
Takardar kudi na NairaHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

To sai dai kuma dimbin bKaashin ya fara kai miliyoyi na 'yan kasar zuwa fuskantar barazana mai girma ga ci gaba da kila ma makoma ta kasar a nan gaba.

Dr Hamisu Yau dai na zaman kwararre ga tattali na arziki, da kuma ya ce kasar na iya fuskantar rikici na tattali na arziki a nan gaba sakamkon dimbin bashin dake ta karuwa a halin yanzu.

Karin bayani: Najeriya: Buhari ya amince da kasafin 2023

Ko bayan talakawa na garin dake fadin an bata, ga su kansu masu kokari na karbar mulkin ta siyasa dai, daga dukka na alamu sabon bashin yai nisa wajen tada hankali cikin kasar.

Abdullahi Wakili dai na takarar zama dan majalisar dattawa a Kaduna da kuma ya ce masu tsintsiyar na neman mai da daukaci na yan kasar zuwa bayin Turai, a bisa hanyar kaiwa ya zuwa ga bukata ta burge da dama.

Babban bankin Najeriya
Babban bankin Najeriya

Ya zuwa ranar yau dai kaso 80 cikin dari na kudade na shiga cikin kasar dai na tafiya ne bisa biyan ruwa kan bashin da ke zaman dabaibayi mai girma.

Kuma a fadar Ladan Salihu da ke zaman kakakin dan takara na jam'iyyar PDP ta adawa a zabe na shugaban kasar, yan lemar na dardar din hawa bisa mulki na kasar a cikin halin bashi na kasar.

Karin bayani: Najeriya: Asarar kudi a kokarin ceto Naira

To sai dai kuma in har ta yi baki ta yi muni a tunani na masu takama da adawar, ga gwamnatin da ke kan mulkin bashin, bashi da illar da wasu a cikin kasar ke ta nuna damuwa kansa a yanzu.

Zainab Ahmed dai na zaman minista ta kudin da kuma ta ce kasar tana da karfin iya kaiwa ya zuwa bashin na ta.