Baraka a hukumar zaben Jamhuriyar Nijar | Labarai | DW | 20.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Baraka a hukumar zaben Jamhuriyar Nijar

Wakilin kungiyar farar Hula ta REPPDD Maikoul Zodi ya yi murabus daga hukumar zaben Nijar, bayan da 'yan adawa da kungiyoyi suka yi kira da su dakatar da ayyukansu a CENI.

Dan takara Issoufou Mahamadou shugaban kasar mai ci da ke neman wa'a di na biyu zai fafata da Hama Amadou wanda a halin yanzu ke kwance a wani asibiti a birnin Paris na kasar Faransa. Sai dai gungun 'yan adawan kasar na COPA da ke goyon bayan dan takara Hama Amadou sun yi kira ga magoya bayansu da su kaurace wa zaben da suka kira jeka na yika.

Sai dai a jajiberin soma wannan zabe, daya daga cikin kusoshin hukumar zaben kasar ta Nijar CENI wanda ake gani shi ne na hudu a hukumar, kuma wakilin kungiyoyin fararar hulla na REPPDD Maikoul Zodi, ya dakatar da ayyukansa daga hukumar bayan da kungiyoyin suka yi kira ga wakillansu da su dakatar da ayyukansu a hukumar zaben ta CENI bisa dalillan da suka kira na saba wa dokokin zabe.