Ban Ki- moon zai kai ziyara Najeriya | Labarai | DW | 21.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ban Ki- moon zai kai ziyara Najeriya

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon zai kai wata ziyara a birnin Abuja da ke Najeriya tare da ganawa da mahukuntan kasar.

Ban Ki-moon

Ban Ki-moon Sakataren Majalisar Dinkin Duniya

Sakataren Majalisar Dinkin Duniyar zai isa birnin Abuja ne a ranar Lahadin nan a inda zai gana da shugaban kasar Muhammadu Buhari tare da ajiye furanni don girmamawa ga wadanda suka mutu sakamakon harin da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai a Abuja.

Kazalika Ban Ki-moon zai kuma tattauna da gwamnoni gami da 'yan kasuwa a yayin ziyarar da zai kai ta kwanaki biyu kamar dai yadda ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta bayyana.

Wannan ziyarar ta Ban Ki moon da zai kai Najeriya na zama ta biyu tun lokacin lokacin daya dare jagorancin hukumar a shekara ta 2007.