Bama-bamai sun kashe rayuka a Najeriya | Labarai | DW | 02.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bama-bamai sun kashe rayuka a Najeriya

Hukumomin a Najeriya sun ce mutane 15 ne suka mutu a wasu hare-haren kunar bakin wake da suka auku cikin wata kasuwar da ke birnin Biu na jihar Borno. Lamarin ya haddasa asarar rayuka tare da jikkatar wasu akalla 60.

A karon afrko an kai hare-haren kunar bakin wake a garin Biu dake cikin jihar Borno ta Najeriya, inda aka samu asarar rayuka da jikkatar wasu masu yawa. Hukumomin kasar sun ce mutane 15 ne suka mutu a hare-haren da suka auku cikin wata kasuwar da ke birnin Biu.

A cewar rundunar 'yan sandan jihar ta bakin kakakkinta Victor Isuku, baya ga wadanda suka mutun, akwai karin wasu mutane kimanin 60 da suka jikkata. Sai dai shaidu sun ce alkaluman wadanda suka mutun sun zarta wadanda jami'an na tsaro suka bayar.

Ya zuwa yanzu dai kura ta lafa a garin, kuma babu wata kungiyar da ta dauki alhakin harin. Sai dai kungiyar nan ta Boko Haram da ta dauki shekaru kusan tara tana kashe-kashe a kasar, na kaddamar da hare-hare masu kama da na wannan Asabar.