Bam ya kashe ′yan gudun hijira 20 a Siriya | Labarai | DW | 17.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bam ya kashe 'yan gudun hijira 20 a Siriya

Harin ya auku ne bayan fashewar bam cikin mota a kusa da birnin Dier al-Zor da ke gabashin kasar, inda wasu mutane 30 suka jikkata.

Ana zargin mayakan I S da kai harin kamar yadda kamfanin dillacin labaran kasar SANAA ta ruwaitoKawo, amma kawo yanzu babu karin bayani daga bangaren gamnati ko ita kuingiyar I S da ake zargi da kai harin, sai dai mumunan harin na zuwa ne jim kadan bayan da sojojin gwamnati suka yi luguden wuta da ya yi sanadiyar mutuwar kananan yara biyar, tare da ma'aikatan ceto biyu a kauyuka da ke keweye da birnin Damascus.Rasha da Turkiya da Iran za su gana kan Siriya

Kwana hudu kenan da yankunan ke cikin matsanancin hali na barin wuta, a wani matakin gwamnati na kakkabe 'yan adawa da ke rike da yankunan. A watan Agusta ta gabata kasashen Rasha da Turkiyya da Iran sun ajiye za a fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta a wasu yankunan Siriyar, ciki har da yankin da sojojin suka kaddamar da luguden wuta a ranar Jumma'a.

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Syrian Observatory for Human Right, ta ce ko a ranar Alhamis sai da 'yan tawayen suka yi ta harba makaman roka a kusa da Damscus wanda ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula 10. MDD ta yi kiyasin mutuwar mutane sama da 300,000 tun bayan fara yakin basasar kasar a shekara ta 2011.Siriya: Gwamnati ta kwaci Deir Ezzor daga IS

 

DW.COM