Rasha da Turkiya da Iran za su gana kan Siriya | Labarai | DW | 16.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha da Turkiya da Iran za su gana kan Siriya

Shugabannin za su gana da Putin a gidansa da ke Sochi inda za su tattauna ci gaban da ake samu a Siriya da ma lamuran da ke faruwa a yankin.

Shugaba Vladimir Putin na Rasha a mako mai zuwa zai karbi bakuncin takwarorinsa na Turkiya da Iran wato Recep Tayyip Erdogan da Hassan Rouhani inda za su yi wani baban taro kan makomar Siriya kamar yadda kafafan yada labarai a kasar ta Turkiya suka bayyana a wannan rana ta Alhamis.

Shugabannin za su gana da Putin a gidansa da ke Sochi inda za su tattauna ci gaban da ake samu a Siriya da ma lamuran da ke faruwa a yankin. Za su kuma gana ne a ranar 22 ga watan nan na Nuwamba a cewar kamfanin dillancin labaran Anadolu a Turkiya.

Yayin da ake ganin Rasha da Iran a matsayinn masu mara baya ga Shugaba Assad ita kuwa Turkiya a watannin baya-bayan nan na sassauta kalamanta kan shugaban inda ta karkata kan Kurdawan Siriya da take kallo a matsayin 'yan ta'adda.