Siriya: Gwamnati ta kwaci Deir Ezzor daga IS | Labarai | DW | 03.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Siriya: Gwamnati ta kwaci Deir Ezzor daga IS

Sojojin gwamnatin Siriya masu samun goyon bayan Rasha sun kwace birnin Deir Ezzor daga hannun mayakan IS a cewar kungiyar da ke sa ido kan kare hakin bil-Adama ta (OSDH) a kasar ta Siriya.

Tun dai a jiya kafofin yada labaran gwamnatin ta Siriya suka sanar cewa akwai babban ci gaba da dakarun gwamnatin ke samu a birnin na Deir Ezzor yanki mai arzikin man fetur da ke gabashin kasar iyaka da Iraki. Sai dai kuma a hakumance gwamnatin ta Siriya ba ta ayyana kwace birnin ba. Hakan dai na kara tabbatar da irin mawuyacin halin da 'yan kungiyar ta IS ke ciki a halin yanzu, inda take ci gaba da fuskantar babban koma baya. 

Kungiyar kare hakin bil-Adama ta kasar ta Siriya mai cibiya a birnin London na Britaniya ta OSDH, ta ce an dakatar da harbe-habe, kuma tuni aka soma ayyukan tone nakiyoyi da 'yan jihadin suka bizne a wurare daban-daban. Sai dai kuma wata majiya ta sojan kasar ta Siriya ta ce sun dai kwace sama da kashi 80 ne na birnin.