Bam ya kashe Sojoji biyar a Yemen | Labarai | DW | 05.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bam ya kashe Sojoji biyar a Yemen

Wani dan kunar bakin wake ya tashi bam da ke cikin mota a birnin Aden da ke yammacin kasar Yemen, an ci gaba da ganin tirnikewar hayaki da karar harbe-harben bindigogi nan take bayan tashin bam din a safiyar Lahadi.

Kawo yanzu dai babu tabbacin wadan da suka kai wannan hari da ya faru a wani shingen bincike da ke kusa da hedikwatar tsaro na gundumar Khor Maksar a birnin Aden.G

Gwamnatin Yemen ta kaurar da babbar tashar jiragen ruwa da ke birnin a shekara ta 2015 bayan da 'yan tawayen Houthi suka karbe iko da babban birnin kasar Sanaa a lokacin yakin basasa.

Sama da mutane 10,000 aka kashe a Yemen tun bayan da mayakan Houthi suka mamaye birnin Aden, wanda ya tilasta wa shugaba Abd-Rabbu Mansour Hadi sauya matsuguni tare da neman agajin Sojojin yaki daga gwamnatin Saudiyya. A yanzu dai dakarun gwamnatin da ke samun goyon bayan Sojojin hadaddiyar daular Larabawa, sun mamaye Aden da nufin maido da shugaba Hadi. 

Wannan hari dai na zuwa ne kwana guda bayan da 'yan tawayen Houthi suka harma makami mai linzami a kusa da filin jirgin sama da ke birnin Riyadh babban birnin kasar Saudiyya, harin da gwanatin Saudiyya ta ce dakarunta sun dakile ba tare da haifar da barna ko asarar rai ba.