Bam ya fashe a wata kasuwa da ke Kano | Labarai | DW | 10.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Bam ya fashe a wata kasuwa da ke Kano

An sake kai hari kan birnin Kano na arewacin Tarayyar Najeriya

Rahotanni daga birnin Kano na Tarayyar Najeriya sun tabbatar da cewa wani bam ya fashe a wata kasuwa mai cike da mutane da ake hada-hada.

Shaidun gani da ido sun ce lamarin ya faru a kasuwar Kantin Kwari lokacin da 'yan kasuwa da masu hulda ke harkokin yau da kullum. Jihar ta Kano tana cikin wuraren da 'yan kubngiyar Boko Haram masu dauke da makamai ke kai hare-hare a yankin arewacin Najeriya. Kawo yanzu babu cikkken bayani kan mutanen da lamarin ya shafa.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Pinado Abdu