1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Baerbock ta tsallake farmakin Rasha a Ukraine

February 25, 2024

Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ta katse ziyarar gani da ido da ta ke yi a yankin kudancin Ukraine, sakamakon bayanan sirrin da suka tabbatar da yunkurin hare-haren Rasha da jirage marasa matuka.

https://p.dw.com/p/4cs0p
Ministar harkokin wajen Jamus  Annalena Baerbock a Mykolajiw na Ukraine
Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock a Mykolajiw na UkraineHoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Minista Annalena Baerbock ta katse ziyarar da ta ke yi a birnin Mykolaiv ba tare da bata lokaci ba tare da neman mafaka a wasu motoci masu sulke da aka tanadar mata tare da sauran 'yan tawagarta, bayan an gano jiragen kasar Rashan marasa matuka na shawagi a sararin samaniyar Ukraine.

Karin bayani: Zelensky ya sha alwashin galaba kan Rasha

Ko a ranar 24 ga watan Fabrairun 2024, sai da tawagar ministar suka ji karar jiniya a yankin Odessa na tsawon mintuna 20 a kusa da masaukin ministar ta Jamus da ke kusancin Ukraine.

Kazalika an jiyo karar fashewar wata nakiya da ba a tabbatar da cewa ko Rasha ce ta harba makamai masu linzami a yankin na Odessa da ke yankin kudancin Ukraine.