Badakalar take hakkin dan Adam a CIA | Siyasa | DW | 10.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Badakalar take hakkin dan Adam a CIA

Shekaru 30 da suka gabata aka amince da yarjejeniyar kare hakkin dan adam a duniya amma wannan bai hana ci gaba da samun rahotannin cin zarafin jama'a ba a kasashen.

A wani binciken da ta yi Kungiyar Amnesty International ta yi wa mutane dubu 21 tambayoyi daga sassa daban-daban na duniya, tun daga watan Mayun wannan shekarar, inda kashi 40 cikin 100 na wadanda suka amsa suka ce a kasashensu da zarar aka kama su ko ma wani irin laifi ne, abin da suke fargaba shi ne cin zarafin da za a yi musu, ko da ya ke fargabar dai ta fi yawa ne a Brazil da Mexico a yayin da a kasashen Siriya da Koriya ta Arewa da Usbekistan salon hukuncin ne yake da tsananin gaske.

A yayin da rahoton ya ce akwai ci gaba a kasashe irinsu Turkiyya, sai dai har yanzu suna kama mutane ba bisa dalilan da suka dace ba, Maria Scharlau kwararriya kan hakkokin jama'a a matakin kasa da kasa ta ba da misali da Najeriya:

Maria Scharlau AI

Maria Scharlau: Jami'a a Kungiyar Amnesty International

"A Najeriya alal misali, kusan kowane ofishin 'yan sanda na da wani dan dakin da ake azabtar da mutane, akwai ma wani rahoto da muka samu cewa a JiharLegas, akwai wani ofishin 'yan sandan, da ke da ruwan batir, da bindigogi da duk wani abun yi wa mutun rauni dai da za a iya tsammani, a wurin ne kuma aka kama wani dan shekaru 16 da haihuwa wanda aka kama dan satar wayar hannu, an daure shi na tsawon shekaru bakwai inda kuma aka rika cin zarafin shi, misali an harbe shi a hannu, an kuma rika daura shi a saman daki kafin bayan shekaru bakwan aka yi mi shi shari'a"

Ganin cewa wannan rahoton ya binciki CIA da kuma 'yan jam'iyyar Demokrats da yawa na ganin cewa bai kamata a kyale wadanda ke cin zarafin al'umma ba idan har ana so a yaki ta'addanci. Shin Turai za ta bukaci a gurfanar da CIA a gaban kuliya? mai magana kan harkokin kasashen waje da kare hakkin dan Adam daga jam'iyyar The Greens ta masu rajin kare muhalli a majalisar dokokin Turai Barbara Lochbihler ta yi karin haske:

"A, wannan ma ni da kai na zan bukaci hakan daga Amirka, amma kuma wannan rahoton zai yi tasiri ma a kanmu mu 'yan Turai, domin babu shakka rahoton ya nunar cewa akwai kasashen Turan da suke cin zarafin a boye, inda suke daure mutane a gidajen kurkukun da suka boye, ko mu mun sani domin a majalisar dokokin Turai, tsakanin shekara ta 2012 da 2013 akwai rahoton da aka wallafa da ya nuna cewa akwai irin wadannan gidajen yarin sirrin a Poland, Romaniya da Lithuaniya kuma ma a kasashe irinsu Sweden da Italiya da Birtaniya da suke sace mutane a boye, shi ya sa dole mu duba mu ga irin rahoton da aka bayar daga nan sai mu san irin matakin da ya dace a dauka."

Majalisar Dinkin Duniya ta yi barazanan daukar tsauraran matakai a kan Hukumar Leken Asirin Amirka ta CIA dangane da yadda ta ke cin zarafin jama'a wajen samun bayanai shin akwai alamun cewa za ta yi wani abun da zai yi tasiri? tambayar da DW ta yi wa John Kornblum ke nan, tsohon jakadan Amirka a Jamus:

"Kai babu wannan ai duk zuzutawa suke yi, akwai ma Jamusawan da ke kokarin cewa ya kamata a gurfanar da su a gaban kuliya, wadannan mutane ne wadanda suke da kishin kasa, kuma suka yi aikinsu yadda ya kamata, bai kamata mu mance Amirka kasa ce da ke mayar da kakkausar martani idan aka kai mata hari, abun da muka yi ke nan bayan harin da Japan ta kai kan Amirka a shekarar1941. Idan aka ce sun wuce gona da iri, wannan daidai ne kuma yana da mahimmanci amma a ce wai laifi ne da za a hukunta bai kamata ba"

Sauti da bidiyo akan labarin