Badakalar cin hanci ta girgiza INEC a Najeriya | Siyasa | DW | 12.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Badakalar cin hanci ta girgiza INEC a Najeriya

Biyo bayan abin kunyar da ake zargin ma’aikatan hukumar zabe mai zaman kanta na karbara cin hanci na sama da Naira biliyan uku, hukumar ta dauki matakai na ladabtarawa inda ta dakatar da ma’aikata 205.

Bankado wanan abin kunya na tonon sililin karbar cin hanci da rashawar da ake zargin ma'aikatan hukumar zaben mai zaman kanta ta Najeriya da yi, a badakala ta Naira biliyan 23 da ake zargin an yi amfani da su don su sauya alkaluman zabe babban ala'amari ne, domin binciken da hukumar ta yi ne ya kai ga kara gano mutane 80 da ta yiwa tambayoyi wadanda basa cikin jerin mutanen da hukumar EFCC ta gano.

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriyar zagon kasa ce dai ta gano cewa akwai tsohon kwamishinan hukumar zaben da wasu kwamishinoni na jihohi biyar sun karbi cin hanci, inda a tsanake aka baiwa kowa kasonsa a jihohi 16 na Najeriyar don su tafka magudi a zaben shugaban Najeriyar na 2015. Hukumar dai ta dakatar da mutane 205 tare da sanya su rinka karbar rabin albashi har sai an kammala bincike. 

Nigeria Wahlen 2011 Bild 2 (DW/Gänsler)

Abinda ya fi daga hankali shi ne yadda aka yi amfani da daya daga cikin kungiyoyin farara hula da ke sa ido a zabe wajen kulla wannan cin hanci, kungiyar mai sanya idannu a kan zabubbuka ta Afrika ta Yamma watau WANEO wacce ta zama ‘yar aike a wannan bakadakala, wacce tuni hukumar zaben ta sanar da soke sunanta a dukkanin al'aummuran zabe.

Abin jira a gani shi ne matakin da fadar shugaban Najeriya za ta dauka a kan sauran ma'aikatan hukumar da aka mika lamarinsu gareta, da ma wasu guda 70 da aka mikawa hukumar EFCC don ci gaba da bincike a lamarin da kwararru ke bayyana cewa sai an jajirce don dakile sake faruwarsa a harakar shirya zabubbuka a kasar.

 

Sauti da bidiyo akan labarin