1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babu ci-gaba akan al´amuran hakkin ´yan Adam a Iraki

November 27, 2005
https://p.dw.com/p/BvJG
Tsohon FM Iraqi Iyad Allawi yayi suka akan keta hakkin bil Adama a cikin kasarsa. A cikin wata hira da jaridar The Observer ta birnin London, Allawi ya ce ba wani ci-gaba da aka samu wajen kare ´yancin dan Adam a cikin kasar. Tsohon FM ya ce hasali ma babu wani canji a yanzu da kuma a lokacin mulkin tsohon shugaban Iraqi Saddam Hussein. Allawi ya ba da misali da yadda jami´an leken asiri ke keta hakkin ´yan Adam a gidajen yari na boye. Ya ce a yanzu haka ma akwai wasu kotuna na ´yan Shi´a dake amfani da dokokin Islama wajen yiwa mutane shari´a sannan a wasu lokutan ma su na ba da umarnin aiwatar da hukuncin kisa. Allawi ya yi gargadin cewa Iraqi ka iya fadawa cikin wani yamutsi. Allawi ya kasance FM wucin gadi a Iraqi bayan hambarad da Saddam Hussein a shekara ta 2003 zuwa watan afrilun wannan shekara.