1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babu alamar tsagaita wuta a Siriya

Ramatu Garba Baba
February 28, 2018

Rahotannin daga Siriya na cewa ana ci gaba da barin wuta a garin Ghouta, tungar karshe da ke karkashin ikon 'yan tawaye, duk da yarjejeniyar da aka cimma na tsagaita bude wuta don isar da kayan agaji ga mabukata.

https://p.dw.com/p/2tS0k
Syrien Blutvergießen in Syrien geht weiter - Hilfsorganisationen können Ost-Ghuta nicht erreichen
Hoto: Reuters/B. Khabieh

Fararen hula da ke rayuwa a gabashin garin Ghouta na cikin matsatsi, da dama na fama da rashin lafiya da kuma karancin abinci da ruwan sha, an dora matsalar kai kayan agajin kan Rasha da ake ganin ba ta daina kai hare-hare a tungar 'yan tawayen ba. A yarjejeniyar tsagaita wutar da aka sanya wa hannu, Rasha ta amince ta daina kai hari kan 'yan tawaye na tsawon wata guda bayan da ta kaddamar da wani munmunan farmaki a yankin a makon da ya gabata. Fararren hula fiye da dubu dari hudu ne ke rayuwa a birnin.

Kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta bayyana takaici kan rashin isar da agaji, inda ta daura laifi kan Rasha da ke taimakon gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad cikin yakin basasan. Rasha a na ta bangaren ta zargi 'yan tawayen da karya yarjejeniyar. Rahotannin na cewa rayuka fiye da goma ne suka salwanta tun bayan ayyana dokar.