1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban sakataren OPEC Sanusi Barkindo ya rasu

Binta Aliyu Zurmi
July 6, 2022

Allah ya yi wa babban sakataren kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta duniya OPEC Dr Mohammad Sunusi Barkindo rasuwa a daren jiya Talata.

https://p.dw.com/p/4DjKM
Generalsekretär der OPEC Mohammad Barkindo
Hoto: Afolabi Sotunde/REUTERS

A sanarwar da shugaban kamfanin man Najeriya NNPC Male Kyari ya fidda da wannan safiyar a shafinsa na Twitter, ya bayyana rasuwar Barkindo a matsayin babban rashi ga iyalansa da ma'aikatan kamfanin NNPC da ma kungiyar OPEC.

Barkindo ya rasu yana da shekaru 63 a duniya, kafin rasuwar sa, marigayin na gab da sauka daga mukaminsa na sakataren OPEC bayan kwashe sama da shekaru shida.

Ana sa ran a gaba a yau ne za a fidda bayanai a game da jana'izarsa.