1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ba za a saka dokar kulle a Shanghai ba

March 23, 2022

Hukumomin birnin Shanghai na kasar China sun karyata jita-jitar sake kakaba dokar kulle kan annobar cutar coronavirus yayin da birnin ke fuskantar barazanar cutar a karo na 6.

https://p.dw.com/p/48tuZ
Bildergalerie | China |  Omicron erreicht Chinas Festland
Hoto: Andy Wong/AP Photo/picture alliance

Jita-jitar dai ta haifar da tururuwar mutane zuwa siyan kayayyakin abinci da na amfanin yau da kullum don shirin ko ta kwana.

Barkewar cutar na baya-bayan nan a cibiyar hada-hadar kasuwancin kasar ya haifar da gudanar da gangamin wayar da kai kan mahimmancin yin gwaji yayin da mutane da dama ke ci gaba da kulle rukunin gidajensu na tsawon kwanaki.

Adadin wadanda suka kamu da cutar a birnin ya haura 1000, sai dai kuma hukumomin na cewa za su ci gaba da daukar wasu matakan da ke da mahimmanci fiye da sanya dokar kulle a birnin.