1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ayyukan wanzar da zaman lafiya a Mali

December 4, 2013

Kasancewar ana cigaba da zaman rashin tabbas a arewacin Mali, MƊD na shirin ƙara wa'adin ayyukan wanzar da zaman lafiya a ƙasar

https://p.dw.com/p/1ASye
Hoto: DW/S. Blanchard

'Yan tawayen abzinawan Mali sun ce sun janye yarjejeniyar tsagaita wutar da suka cimma da gwamnati, kuma don haka sun cigaba da jagorancin yankin arewacin ƙasar wannan lamarin dai ya jefa ƙasar cikin wani yanayi na tsaka mai wuya kasancewa rundunar sojin ƙasar da ma gwamnatin ita kanta, ba su da ƙarfin ikon da suke buƙata wajen shawo kan wannan matsalar.

Daga farkon watan Nuwamban da ya shige ne, Faransa, ƙasar da ta yi wa Malin mulkin mallaka ta ƙara dakarunta a ƙasar, kuma tun daga farkon wanan shekarardakarun horaswar Turai na EUTM ke ƙasar kuma bugu da ƙari tun lokacin bazara rundunar ƙasa da ƙasa ta wanzar da zaman lafiya ta MINUSMA ke ƙasar.

Bert Koenders manzon Majalisar Ɗinkin Duniya na musamman a Mali kuma shugaban rundunar ta MINUSMA zai ziyarci Berlin a wannan makon kuma a tattaunawar da yake yi da gwamnatin Jamus, ya shawarce ta da ta tura dakarunta cikin ƙawancen na MINUSMA saboda Majalisar Ɗinkin Duniya za ta ƙara wa'adin aikin sojojin a Mali da shekara guda daga farkon shekarar 2014.

Ayyukan dakarun Jamus a Mali

Matthias Reichenbach ya na tuƙa ɗaya daga cikin jiragen yaƙin da Jamus ta turawa MINUSMA a Mali. Wannan jirgin na ɗiban dakaru da kayayyakinsu da kayan abinci kuma sauran naurorin da suke buƙata alal misali janareta amma kuma banda makamai kuma ya yi ƙarin bayani dangane da aikin da suke yi:

Mun zo nan Mali ne domin mun kula da jiragen saman Majalisar Ɗinkin Duniya a ƙarƙashen ƙudurinta na MINUSMA, tare da sauran dakarun da suka fito daga ƙasashen Afirka daban-daban domin su taimaka wajen daidaita matsalar da Mali ke fama da shi. Aikinmu a nan ya shafi ɗaukan kayayyaki da mutane zuwa yankin arewacin Malin.

Irin waɗannan jirage biyu ne ke kai kawo a cikin Mali a yanzu haka, na ukun yana sansanin dakarun Jamus dake Dakar Senegal, kuma zai yi aiki ne kaɗai idan ɗaya daga cikin wancan biyun ya lalace. Aikin na Mali babban ƙalubale ne ga mutane da kuma kayayyaki a cewar leftanan Odo Wolbers wanda ke jagorantar dakarun Jamus na Malin a MINUSMA

Mali Bundeswehr in Koulikoro
Dakarun Jamus na Bundeswehr a KoulikoroHoto: DW/S. Blanchard

A duk lokacin da ake amfani da jirage, akan sami matsaloli amma abin da yake banbanta na Mali shi ne zafin ranar da ƙasar ke da shi, wannan zafin ranar yana tasiri kan naurorin dake cikin jirgin saboda haka sai mun kunna shi da wuri domin ya daidaita da yadda muke so ya yi aiki, kowace sa'a zafin ranar ke ƙaruwa saboda haka bamu iya yin amfani da shi sosai, a ɗaya ɓangaren kuma ranar farko ta kan kasancewa dakarun da wahala, mussaman idan suka fito Jamus lokacin da ake sanyin hunturu, sai dai a kwanaki uku zuwa huɗun farko dole ne su yi taka tsantsan su riƙa shan ruwa a kai-a kai

Tallafin da Mali ke buƙata

Manzo na musamman na Majalisar Ɗinkin Duniya da MINUSMA Bert koenders ya san mahimmancin damawa da dakarun sojin Jamus, kuma yana fatan ganin Jamus ta ƙara wa'adin dakarunta, ko kuma ma ta faɗaɗa ayyukanta a cikin Mali

" A gani na yana da mahimmanci domin Mali ba ta da wata tazarar kirki daga nahiyar Turai, matsalolin Lampedusa, da matsalolin kaifin kishin addni, alaƙar dake tsakanin tsaro a cigaba a wannan yankin baki ɗaya abu ne dake da dangantaka da Turai da ma Jamus"

Bert Koenders yana so a sami yanayi na cuɗe ni in cuɗe ka tsakanin ƙasashen Turai da kuma ƙungiyoyin wanzar da zaman lafiya a shekara mai zuwa, yadda ta haka za a koma ga daidaito da sulhu ta yadda ba Mali kaɗai ba har ma da 'yan sanda da masu tabbatar da tsaro kan iyakoki za a gyara a kuma haɗa kai da ƙasashen Afirkan dake maƙotaka da ita.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Umaru Aliyu