Ayyukan bugon hatsi na kashen kaka a Damagaram | Zamantakewa | DW | 09.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Ayyukan bugon hatsi na kashen kaka a Damagaram

Farfado da al'adar kimshe ko bugon hatsi da kulake da ke zaman ayyukan karshe na manoma a wani mataki na adanon hatsin da suka samu cikin gonaki.

Yankin Damagaram na Jamhuriyar Niger manoman tudu sun farfado da wata dadadiyar al'ada tun ta iyaye da kakani, inda samari matasa daga garuruwan karkara ke shirya gayyar aikin kimshe don samun taimakon jama'ar karkara domin kaucema mamayar dobobin makiyaya a daf da tatare albarkar daminar da suka samu. Samari majiya karfi ne dai da ake gayyatowa daga garuruwa makusanta na karkara ke bugon hatsi da kulake da ake kira kimshe, kuma suna wannan aiki ne cikin annashuwa da nuna kaunar aikin ganin cewa gayyar na iya zuwa ne ga kowa, musamman ma wadanda suka samu albarkar damina mai yawan gaske cikin gonakinsu. Wanan dadadiyar al'ada dai da manoman tudu suka gada tun iyaye da kakanni na a zaman wani mataki na taimakekeniya a aikin gona a cewar Malam Suleymane daya daga cikin dattawan garin Gobro Bugaje da 'yan kimshe ke kira da koren konce...

" Idan an kare kala, kuma an yi rumbuna, kowa ya shirya, sai a yi kira zuwa ga kimshe. To idan aka zo ana cika sanho ne makil a zuba cikin rumbu, haka-haka sai yi guda tara (09) sannan a fitar da daya a matsayin wanda za'a bayar sadaka kamar yadda tsarin yake. Kuma dalillan da suka sa ake bugon hatsin da kulake, don idan aka kwashe hatsin ba tare da an buga shi ba to rumbun ba zai dauki hatsi mai yawa ba, sannan suma mata masu sussuka abun na zo musu da sauki."


Daga garuruwan Madatai, Kadamari, Gobro Bugaje, garin Natirje, har ya zuwa Efadalam cikin jihar ta Damagaram, manoman na amfani da wanan dama ta gayatar jama'a wajen kimshe kamar yadda su Malam Abdura'uf shugaban yan kimshe ke cewa:

" Idan muna wannan aiki sai hannayanmu suna ruwa sabo wahala, sannan kuma ga kay-kay da ke addabar jikinmu, kuma wasu na tafiyar mintuna 40 a kasa kafin su iso wurin wannan aiki na kimshe, kuma idan aka buga hatsin to rumbun da zai dauki sanho 40 wanda ba'a buga ba, zai iya daukan sanho 80 da aka buga. don haka wata dubara ce ta samun adano na hatsi mai yawa cikin rumbu guda."

Shi dai wannan aiki na gayyar kimshe, ya shafi maza da mata, har ma da yara matasa, domin kowa daga ciki na da iri-irin ayyukan ta ya kan iya yi. Musali mata, suka yin rakar baga idan an kammala, ma'anna su yi amfani da mararaki domin fidda tsabar hatsin da ta shiga cikin kasa. Kuma idan mace ta raki musali ma'awni goma na hatsi sai a bata ma'awni uku daga ciki, shi kuma mai hatsin ya dauki ma'awni bakoye. Don haka ayyukan Kimshe aiki ne wanda duk da irin wahalar da ke cikinsa amma kuma masu yinsa na samun wani dan sakamako amatsayin wani dan abun kara kwarin gwiwa.