Asusun IMF zai tallafa wa Najeriya | Labarai | DW | 04.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Asusun IMF zai tallafa wa Najeriya

Tattaunawar ta mahukuntan Najeriya da Asusun IMF na duba yadda za a sake mai da Najeriya bisa turbar bunkasar tattalin arziki.

Nigeria Symbolbild Muhammadu Buhari Anti-Korruptions-Offensive

Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai gana da shugabar Asusun ba da Lamuni na IMF a ranar Talata mai zuwa a dai dai lokacin da kasar ke tunkarar matsalar tattalin arziki bayan da farashin man fetir da kasar ke dogaro da shi a duniya ke yin kasa.

A cewar asusun na IMF Christine Lagarde za ta gana ne da shugaba Buhari da ministar kudin kasar ta Najeriya Kemi Adeosun.

A cewar Lagarde tattaunawar za ta mayar da hankali kan tattalin arziki da ma koma bayan da farashin man fetir ke samu a kasuwar duniya.

Babu dai karin bayani kan wasu batutuwa da tattaunawar za ta tabo sai dai ana ganin za ta kewaye batun kokarin da gwamnatin Shugaba Buhari ke yi ne na sake mayar da Najeriyar bisa turba a matsayinta na mai karfin tattalin arziki a Afirka.