Arangamar 'yan sanda da masu bore a Legas | Labarai | DW | 12.06.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Arangamar 'yan sanda da masu bore a Legas

Yayin da Najeriya ke bikin ranar dimukuradiyya, masu zanga-zangar adawa da gwamnati sun yi artabu da jami'an tsaro a Legas da Abuja, an kama na kamawa wasu jikkata bayan tarwatsa su da hayaki mai sa hawaye.

Masu zanga-zangar na nuna fushinsu kan rashin tsaro a Najeriyar musamman yawaitar satar mutane don neman kudin fansa da kuma kungiyoyin ta'addanci da ke addabar kasar.

Wannan daiu na zuwa ne bayan da 'yan bindiga sun kashe akalla mutane 53 a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin kasar, kamar yadda 'yan sandan jihar suka tabbatar.

Mahara kan babura sun bude wuta kan manoma a kauyukan Kadawa da Kwata da Maduba da Ganda Samu da Saulawa da Askawa a guddumar Zurmi.

Zamfara dai na cikin jihohin arewacin Najeriya da ke kuka da rashin tsaro na masu satar mutane, inda ko a baya-bayannan gwamnan jihar ya tube kwamishinoni da wasu kusohin gwamnatinnsa saboda rashin tsaron.