Arangama a tsakanin tsagerun yakin sa kai a kasar Somalia | Labarai | DW | 11.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Arangama a tsakanin tsagerun yakin sa kai a kasar Somalia

Sojin sa kai na musulmai da kawancen madugan yaki a Somalia na ci gana da dauki ba dadi da juna, a kokarin da suke na kwace babban birnin kasar wato Magadishu.

Wannan dauki ba dadin dai na faruwa ne duk kuwa da yarjejeniyar tsagaitawa da bude wuta da aka cimma a tsakanin bangarorin biyu a jiya laraba.

Rahotanni da suka iso mana na nuni da cewa ya zuwa yanzu sojin sa kann musulmin na rike ne da kashi 80 cikin dari na birnin na Magadishu.

A dai dauki ba dadin daya faru a jiya laraba, an tabbatar da cewa mutane 13 ne suka rugamu gidan gaskiya, wasu kuma da dama suka jikkata.