Annobar cutar bakon dauro a Turai | Labarai | DW | 28.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Annobar cutar bakon dauro a Turai

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ko OMS ta yi gargadin yiwuwar bullar annobar cutar bakon dauro a wasu kasashen Turai sabili da karancin allurar rigakafin kamuwa da cutar a wasu kasashe bakwai na nahiyar.

 Hukumar Lafiyar ta Duniya ta bayyana hakan ne a ranar Talatar nan inda ta ce yanzu haka an samu mutane sama da 500 da suka kamu da cutar ta bakon dauro a watan Janerun da ya gabata a wasu kasashen nahiyar da suka hada da Faransa da Italiya da Switzerland da Jamus da Poland da Romaniya da kuma Ukraine wadanda a halin yanzu suka kasa yi wa kashi 95 daga cikin dari na al'ummarsu allurar rigakafin kamuwa da cutar.

Tuni ma dai cutar ta kashe mutane 17 tun daga watan Janerun bara a kasashen Roumania da Italiya inda mutane 283 suka kamu da ita. Mutane sama da dubu 134 dai wannan cuta mai saurin yaduwa ta kashe a fadin duniya a shekara ta 2015 musamman yara 'yan kasa da shekaru biyar.