1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zargin siyan katunan zabe daga hannun jama'a

December 13, 2022

Hukumar zaben Najeriya ta baiyana damuwarta kan yadda wasu 'yan siyasa ke kokarin amfani da kudi don siyan kuri'un jama'a a yayin da aka fara rarraba katunan zabe.

https://p.dw.com/p/4Ksao
Hoto: Stefan Heunis/AFP

Daya daga cikin kalubale na gudanar da zabe mai inganci a Najeriya a wannan lokacin shi ne batun amfani da kudi ga masu zabe, wannan ya sa shugaban hukumar zabe na kasa Farfesa Mahmud Yakubu, ya koka da yunkurin amfani da kudi ga 'yan kasa masu zabe a 2023.

Amfani da kudi ta kowace siga a siyasar Najeriya ba sabon labari bane, amma a wannan lokaci da hukumomi ke ikirarin gudanar da zabe cikin adalci ga kowa da kowa, wannan batu na mai karfin kudi ka dauka, ya zama tamkar kadangaren bakin tulu a siyasar Najeriya. 

A baya bayan nan, rade-radin ya baza gari cewa, matakan da babban bankin kasa ya dauka na sauya fuskar kudaden kasar na da nasaba da dakile kokarin 'yan siyasa na amfani da kudade a zaben kasar na 2023 da ke tafe. Jama'a da dama sun bayyana ra'ayinsu kan wannan anfani da kudi ta barauniyar hanya a cikin jihohin kasar talatin da shida, ciki har da Abuja, babban birnin kasar.