Ana zaben raba gardama a gabashin Ukraine | Labarai | DW | 11.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana zaben raba gardama a gabashin Ukraine

'Yan waren gabashin Ukraine masu goyon bayan Rasha na gudanar da zaben raba gardama kan makomar yankin

Ana zaben raba gardama cikin yankuna biyu na gabashin kasar Ukraine, kan ci gaba da zama karkashin mahukuntan birnin Kiev ko samun kwarya-kwaryar 'yanci, zaben da yake cike da cece-kuce da tir daga kasashen Yammacin Duniya. Ana gudanar da zaben cikin makarantu, kuma tuni wasu mutanen suka kada kuri'a, wadda ake gani ta yanke kauna ce wa Ukraine.

Shugaban gwamnatin wucin gadi na kasar ta Ukraine Oleksander Turchinov ya gargadi 'yan aware masu goyon bayan Rasha da ke Donetzk da Luhansk kan mummunan sakamakon da za su fuskanta bisa zaben.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Shugaban Faransa Francois Hollande da ke ziyara a nan Jamus, duk sun yi watsi da zaben raba gardama na gabashin Ukraine, wanda suka ce ya saba ka'ida. Zaben na wannan Lahadi ya tusa tsaron yuwuwar barkwwar yakin basasa. A wannan Asabar da ta gabata an yi musanyen wuta tsakanin sojoji da 'yan aware.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu