1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Moroko ke bayar da umarnin yin bulaguro ga 'yan kasa

Ramatu Garba Baba
November 2, 2018

Gwamnatin Moroko ta bijiro da wani sabon tsari, inda ake bukatar matafiya su cike takardar neman amincewar gwamnati kafin barin kasar zuwa wata kasa a yunkurin magance matsalar kwararan 'yan cirani.

https://p.dw.com/p/37ZPo
Spanien hunderte Migranten haben den Grenzzaun von Ceuta erstürmt
Hoto: Getty Images/A. Koerner

Daga yanzu matafiya za su cike wani fom ta yanar gizo sannan su jira har sai gwamnati ta yi na'am kafin barin kasar. Dokar ta shafi duk 'yan kasar da kuma kasashen yankin Afirka da al'ummarta ke da izinin shiga Moroko ba tare da takardar Visa ba, matafiya na bukatar akalla kwanaki hudu kafin samun izinin yin bulaguro.

Ana ganin matakin zai taimaka wajen sanin wa ya shiga wa ya bar kasar,  da ke fuskantar tsananin matsi a yunkurin da ake na shawo kan kwararran 'yan gudun hijira da suka mayar da Moroko kafar da ake dafawa don shiga nahiyar Turai.'Yan gudun hijira akalla dubu arba'in ne suka yi nasarar shiga kasar Spaniya daga Moroko tun daga farkon watan Janairun wannan shekarar ta 2018.