Ana mummunan yaki a Aleppo | Labarai | DW | 08.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana mummunan yaki a Aleppo

Yaki na kara rincabewa a birnin na biyu mafi girma a kasar Siriya, inda sojojin gwamnatin ke kai faramaki ta sama da ta kasa, a wani yunkuri a yita kare.

Fadan da ake yi a Aleppo ya yi sanadiyzar kwarar 'yan gudun hijira dubbai, inda yanzu haka suke fake a kan iyakar Siriya da Tuirkiya. Yayin da ake cewar Rasha na azawa sojan Siriya a yakin da 'yan tawaye, ita ma Saudiyya ta sanar da shirin tura sojojinta, a wani abin da suka ce yakar kungiyar IS ne, sai dai ganin yadda Saudiyya ke tallafa wa 'yan tawaye da kudi da makamai, hakan ya sa gwamnatin Siriya ta yi gargadi mai karfi kan shirin na Saudiyya, inda ministan harkokin wajen Siriya, Walid Mualem ya bayyanan cewa.

"A hir duk wani ya yi tunanin kai hari a Siriya ko kuma ya keta yancin kasar, da nufin tura dakaru ba bisa izinin gwamnati ba. Ina tabbatar muku duk wata tsokala tawannan hanyar to kasar da ta tura sojojin ta tabbatar za a mayar mata da sojojin cikin akwatanan gawa., walau Saudiyza ce ko Turkiya"