1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana kazamin fada tsakanin Ukraine da Rasha

Mouhamadou Awal Balarabe
June 9, 2023

A daidai lokacin da ake fada mai tsanani a kudancin Ukraine, Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya ce kyiv ta gaza kai labari a farmakin da ta shafe makonni tana shiryawa duk da taimakon da ta samu daga kasashen Yamma.

https://p.dw.com/p/4SPLN
Birnin Ternopil na Ukraine na daga cikin wuraren da rasha ta kai hariHoto: State emergency service of Ukraine/REUTERS

Sojojin Rasha sun nunar da cewa suna gwabza kazamin fada da dakarun Ukraine a kudancin kasar bayan da suka dakile hare-hare da aka kai musu a biranen da suka mamaye. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da shugaba Rasha Vladimir Putin ya ce Ukraine ta fara kai farmaki da ta dauki lokaci tana shirya, amma kuma ba ta yi nasara ba.

Sai dai Putin ya yarda cewa har yanzu sojojin Ukraine na da karfin illata abokan gaba sakamakon kayan aiki na zamani da kasashen yammacin duniya suka samar mata. Dama dai Amirka ta sanar da wani sabon kaso na dala biliyan 2 na taimakon soji ga Ukraine, wanda ya hada da na'urorin kare kai daga hare-haren jiragen sama da kuma harsasai.

Har yanzu hukumomin Ukraine ba su tabbatar da kaddamar da farmakin da suka shafe watanni suna shiryawa ba.