1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Libiya: Fataucin kodar 'yan Afirkan da ake garkuwa da su

Mahmud Yaya Azare ZMA
June 11, 2026

Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun koka kan halin da baƙin haure da 'yan ci rani ke ciki a Libiya, sakamakon yadda fatauci da sanssanan jikinsu ke bunkasa a kasar.

https://p.dw.com/p/5FDrd
Niger Agadez 2017 | Westafrikanische Migranten nach Flucht aus Libyen auf Rückweg
Hoto: Issouf Sanogo/AFP

 Kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa na nuna matukar damuwarsu kan halin da baƙin haure da 'yan ci rani ke ciki a Libiya, sakamakon yadda fatauci da sanssanan jikinsu ke bunkasa a kasar da kungiyoyin asiri da na fasa kwabrin bil adama ke cin karensu babu babbaka saboda raunin gwamnati.

Wani sabon binciken da aka fitar a wannan makon na nuni da cewa, fataucin sassan jiki a Libiya ya zama wata sabuwar sana,a da kungiyoyin asiri da masu fasa kwabrin bil adama ke karaa ingantawa, yadda kuma galibin bakin hauren ke fadawa cikin komarsu, a yayin da suke hankorar keta Teku zuwa Turai.

Lamarin da ke zama wani babban kalubale da ke buƙatar haɗin gwiwar duniya baki ɗaya don ceto rayukan dubban mutane da ba su san hawa ko sauka ba, wadanda ake ci gaba da ci da guminsu. A sabon Rahoton da ta wallafa mai taken, "Fataucin kodar 'yan Afirkan da ake garkuwa da su a Libiya", bayan sun kasa biyan kudin fansa.

Libyen Tripolis 2015 | Festgenommene afrikanische Migranten im Auffanglager in Tripolis I Gesichter verpixelt
Hoto: Hazem Turkia/AA/picture alliance

Kungiyar binciken kwakwaf ta Think Tank da ke kasar Birtaniya, ta sanar da cewa hatsarin da masu hankoran zuwa Turai ta barauniyar hanya ke fuskanta a Libiya, na fatauci da sassan jikinsu musammama koda, ya dara nesa ba kusa ba irin bala'in igiyar ruwan da ke halaka dubun dubatan 'yan ci rani a da ke yankar Teku zuwa Turai duk shekara.

Thomas Ladder kakakin kungiyar ne da ta gano cewa, a tsukin shekaru biyun da suka gabata, kimanin bakin haure 300 da ke tsare a hannun gungun kunggiyoyin masu tafka ayyukan ta'asa aka yiwa fidar cire koda,bayan da iyayensu suka kasa biyan kudin fansarsu:

"A madadin cimma burinsu na samun rayuwa ta gari, sun tsinci kansu cikin rayuwar tsananin azaba.Wannan shi ne halin da wadannan bayin Allah da aka cirewa koda karfi da yaji ba da son ransu ba ke rayuwa a Libiya. Cikin fargabar sake cire musu wasu sauran gabban jikin nasu, kafin jami'an tsaron gwamnatin Libiya da MDD ta aminta da halaccinta su yi nasarar kwatosu daga hanun miyagun."              

Yusuf Warfali, daya daga cikin ma'aikata a tawagar binciken kwakwaf din ya ce, galibin wadanda aka fi cirewa kodar 'yan Nahiyar Afirka ne saboda da an canfasu a kan cewa, gabobinsu sun fi ingancikamar yadda wadanda ake cire musu gabban ba su galabaita:

"Yawancin wadanda ake cirewa kodar 'yan nahiyar Afirka ne. A kan kuma basu kula ta musamman kafin a yi musu fidar cire kodar. Amma da zarar an gama sai a yi watsi dasu a barsu su yi ta shan fama.Wasu ma hakan ne ke musu sanadiyyar mutuwa.Galibin wadanda muka gana da su sun ce mana, sun gwammace sau dubu da zama a kasashensu, duk da yake yake da talauci da rashin aikin yi da suke fuskanta a cikinsu."

Griechenland Lawrio 2025 | Griechische Küstenwache sammelt Migranten nach Ankunft
Hoto: Aris Messinis/AFP

Uthman Dabibah dan kasar Sudan ne da aka cirewa kodar bayan da iyayensa suka kasa turo kudin fansarsa:

"An tsaremu cikin wani wuri ne mai matukar duhu a cunkushe. Sau daya ake bamu gurasa da ruwa. A kan tambayemu a kai a kai kan mu bada nambobin danginmu da za,a kira don biyan kudin fansa. Sun ce mana duk wanda ba a turo mar kudin fansa ba za su cire mar koda. Ni nayi sa,a na tsira da raina bayan da aka cire min kodar. Akwai wata mata da danta dan shekaru kimanin 12, bayan da aka dawo damu aka jefar ita a ranar ta mutu, shi kuma danta ya mutu washe gari."

A yanzu, ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa suna kira ga matasan Afirka da su kiyayi bin hanyoyin fasa-kwauri, a daidai lokacin da suke matsa lamba ga gwamnatoci don ladabtar da duk likitoci da masu laifi da ke da hannu a wannan aika aikar.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani