1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana fafatawa a zaben Najeriya

February 23, 2019

A yau ne ake zaben kasa a Najeriya, inda shugaba mai ci ke neman wa'adi na biyu. Tuni aka fara kada kuri'u don sama wa kasar sabbin jagorori.

https://p.dw.com/p/3DwPn
Kombobild Muhammadu Buhari und Atiku Abubakar

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na fuskantar babban kalubale daga dan takarar jam'iyyar PDP mai hamayya, Atiku Abubakar, a kokarin neman wa'adi na biyu na mulki a zaben da ake shirin farawa a yau Asabar.

Takarar shugabancin Najeriyar, kasa mai karfin arziki a nahiyar Afirka ya yi kusa matuka da ke wahalar bayyana wanda zai lashe shi kai tsaye a tsakanin shugaban mai ci, da kuma Atikun, wanda dan kasuwa ne kuma tsohon mataimakin shugaban kasa.

Dama dai a makon jiya ne aka tsara gudanar da zaben, amma aka dage 'yan sa'o'i gabanin fara shi, abin kuma da wasu ke ganin ta yiwu hakan ya shafi kuzarin jama'a na fitowa don kada kuri'a.

Hukumar zaben kasar ta ce an dage zaben ne a makon na jiya, saboda matsalolin da suka danganci jigilar kayayyakin zaben.

Najeriyar dai na fama da matsaloli da suka hada da na tsaro da kuma karuwar marasa ayyukan yi, da kuma ke ci gaba da yi wa tattalin arzikin kasar barazana.