Ana cigaba da tashe-tashen hankula a Iraki | Labarai | DW | 17.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana cigaba da tashe-tashen hankula a Iraki

Mutane da dama sun mutu a wasu tagwayen hare-hare a wata unguwar 'yan Shi'a da ke birnin Bagadaza.

Fiye da mutane 44 ne aka hallaka a wasu tagwayen hare-hare da a Iraki. Alkalumman da mahukunta suka bayar na cewa akalla mutane 90 kuma sun samu raunuka a hare-haren guda biyu da aka kai a unguwar Al-Shaab inda akasari 'yan Shi'a ke zaune da ke a arewacin Bagadaza babban birnin Iraki. Wani mai magana da yawun ma'aikatar cikin gida ya ce daga cikin wadanda suka kai harin kunar bakin waken har da mace guda. A kwanakin da suka wuce dai an fuskanci munanan hare-haren a Iraki wanda kungiyar IS mai da'awar kafa daular Islama ta dauki alhakin kaiwa.