Ana ci gaba da yakin neman zabe a Nijar | Siyasa | DW | 01.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ana ci gaba da yakin neman zabe a Nijar

Shugaban Nijar Mahammadou Issoufou ya yi ikrarin iya lashe zaben shugaban kasa na ranar 21 ga wannan wata na Fabrairu tun a zagayen fako. Sai dai 'yan adawar kasar sun ce batun nasa tatsunniya ce

A Jamhuriyar Nijer 'yan takara na ci gaba da yakin neman zaben shugaban kasa wanda za a yi a jumulce da na 'yan majalisar dokoki a ranar 21 ga watan Fabrairu da muke ciki. Kuma a wani bukin kaddamar da jadawalin aikinsa da yake son yiwa 'yan kasa idan sun sake zaben sa a wanni waadi na shekaru biyar, dan takarar jamiyyar Pnds Tarayya mai mulki Shugaba Issoufou Mahamadou ya ce bai ga abin da zai hana masa shallewa a wani waadin mulki ba tun daga zagaye na farko ganin irin yadda shekaru biyar na waadin mulkinsa suka samu karbuwa daga alummar kasar

"Za mu lashe zaben nan tun a zagaye na farko saboda maimakon jiran har sai an kai ga waadi na biyu don kulla kawance tsakaninmu da jamiyyun siyasa kamar yadda aka saba, to mu mun kulla yarjejeniyar tun a zagayen farko", In ji Shugaban kasa Issoufou Mahamadou dan takarar Jamiyyar Pnds Tarayya mai mulki a yayin bukin kaddamar da mahimman manufofin da ya saka a gaba idan har jamaa suka sake zaben shi a wani sabon waadi na shekaru biyar masu zuwa.

Dan takarar na Jamiyyar Pnds Tarayya ya bayar da hujjojinsa uku ne yana mai cewar ta dalilinsu ba zai taba faduwa zaben da ke tafe ba a ranar 21 ga wannan watan ganin yadda tun daga farko dan takarar ya kulla yarjejeniya da wasu jamiyyu kimanin 40 da wasu daga cikinsu suka dakatar da takararsu ta shugabancin kasa, baya ga ayyukan da ya yi da ya ce sun kasance na gari ga 'yan kasa ganin yadda alkawurran da ya dauka na aiki ya zartar da sama da kashi 94 daga cikin dari, kana ga wani sabon alkawalin da ya dauka don kara inganta rayuwar ta 'yan kasar ta jamhuriyar Nijer.

Jam'iyya mai mulki na goyon bayan kalaman shugaban kasa

Kalamun dai na ci gaba da daukar hankali tun daga ranar da shugaban ya furta su. To amma a ganin 'ya 'yan jamiyyarsa ta Pnds Tarayya shallewa tun daga zagayen na farko da shugaban kasa ya ce ba abin mamaki ba ne. Alhaji Assoumana Malam Issa kakakin Jamiyyar Pnds Tarayya ne:

Ya ce "To lisafa duk wadannan ayyukan da shugaban kasa ya yi da duk jamiyyun nan da suka ce tun a zagaye na farko za su kama wa shugaban kasa da talakawan da suka yarda da shugaban kasa da Pnds Tarayya, kenan irin wannan shugaban kasa talakawa sun gano da shi kuma suna alfahari da shi kuma suna bugun gaba da shi da cewar ba su taba samun shugaban kasa kamar shi ba kenan idan har irin wannan shugaban kasar ya dawo ba za su taba cewa idan ya tambayi kuriarsu su hana shi ba don haka tun zagaye na farko za ya wuce a ranar 21 ga watan febraru"


Seini Oumarou Kandidat Wahlen im Niger

Ko baya ga 'ya 'yan jamiyyar ta Pnds Tarayya mai mulki wasu abukanin kawancen jamiyyar na ci gaba da zuga shugaban kasa da wani kirarin da 'yan adawa suka ce shi ne irinsa na farko da suka taba ji a tarihin siyasar Nijer:

Ya ce "Muna tare da kai ka yi masu kayin tsaye kayin reni kayin da ba a shan fansa tai har su gigice"

'Yan adawa a Nijar sun ce kalaman shugaban kasa na tatsunniya ce

Sai dai tuni abokan hammayar shugaban kasar da suka yanke hukuncin kalubalantar shi suka fara sukar kalaman zarcewar dan takarar tun daga zagayen farko na zabe. Alhaji Tahiru Gimba dan takarar Jamiyyar Model Maaikata ne a zaben shugabancin kasa:

Ya ce "Ai aka ce idan har mai fadi ba ya da hankali ai shi mai saurare ya yi ma kansa hankali. Kenan sai a roki Allah don ya maido da hankalinsu don su san da cewar iko Allah yake bayar da shi kuma yana iya amshe shi yadda ya ga dama don shi ke ba da shi kuma shi ke karbar shi. To idan da Tandja bai fidda man fetur ba ta kaka zaa wani aiki"

Shima dai dan takarar a karkashin inuwar jam'iyyar RSD Gaskiya da ya kasance tare da shugaban a waadinsa na farko kuma ya kudri anniyar kalubalantar sa cewa ya yi matakin da shugaban yake son yi a yanzu abu ne da baa taba gani ba a Nijer saboda hakan ta kan yiwu ya zamannto lisafin duna kawai. Alhaji Shehu Amadou dan takarar shugaban kasa ne a zaben na wannan shekarar

Ya ce "Wannan ka san dai da akwai kirarin zabe na siyasa kuma kowa yana da irinshi wannnan tunda aka fara siyasa a Nijer zaben shgaban kasa bugu na biyu ake kuma ban ga abin da ya sake a cikin jamiyyun siyasa ba zuwa yanzu da zai sa a ce hakan za ta kasance a yanzu".

Komi take ci dai fagen siyasar Nijer na kasancewa ko da yauce tamkar mace mai ciki ganin yadda yake bayyana wasu lokutta da ababe irin na ban mamaki wannan fatar na a matsayin wani sabon babi da yekuwar zaben 2016 ta bude da shi a tsakanin 'yan takarar zabe na adawa da masu rinjaye

Sauti da bidiyo akan labarin