Ana ci-gaba da kidayar kuri´u na zaben shugaban kasar Haiti
February 11, 2006Talla
Sakamakon baya bayan nan da aka bayar na zaben shugaban kasar Haiti ya nuna cewa tsohon shugaban kasa Rene Preval na gaba da yawan kuri´u fiye da kashi 50 cikin 100. Hakan dai ya dan dara yawan rinjayen kuri´un da yake bukata don kauracewa zuwa zagaye na biyu na zaben a cikin wata mai zuwa. Bayan an kammala kidayar kimanin rabin kuri´un da aka kada a zaben na ranar talata, babban mai kalubalantar Preval kuma shi ma tsohon shugaba, Leslie Manigat na da kashi 11.4 cikin 100. Ana ganin Preval a matsayin dan goyon bayan tsohon shugaba Jean-Bertrand Aristide. Zaben dai shi ne na farko tun bayan hambarad da Aristide shekaru biyu da suka wuce kuma ya fice daga kasar.