1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Magance matsalar ruwa na bukatar hada karfi

Uwais Abubakar Idris AH/SB
March 22, 2023

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Najeriya ya kadammar da rahoton albarkatun ruwa na wannan shekara a Abuja, inda ya bukaci hada hannu da gwamnati da ma mutane domin shawo kan kalubale na rashin ruwa.

https://p.dw.com/p/4P5F3
Najeriya I Cutuka sakamakon matsalar ruwan sha
Matsalolin ruwan sha a NajeriyaHoto: Gilbertson/Zumapress/picture alliance

Hukumomin Majalisar Dinkin duniya ne suka hadu da na ma'aikatar ruwa da albarkatun kasa na Najeriya a kasa batun samar da ruwan sha ga jama'a, wanda shine kuduri na shida na ci-gaba mai dorewa na Majalisar Dinkin Duniya watau samar da ruwan ga kowa nan da shekara ta 2030. Sun kadammar da rahoton ruwan na wannan shekara inda aka duba inda wannan rahoto da shafi Najeriya musamman karancin tsaftaccen ruwan sha da al'ummarta ke fuskanta wanda ke barazana da lafiya da batun samar da abinci ga kasa. Rahoton da ya bukaci hanzarta samar da chanji domin shawo kan matsalolin ruwa da kula da muhalli.

Najeriya I Ruwan sha
Ruwan sha a NajeriyaHoto: Emmanuel Arewa/AFP/Getty Images

An dai kadammar da rahoton ne lokacin da asusun na Unicef ya bayyana fargaba a kan yara milyan 78 da za su fuskanci matsalolin da suka shafi karanchin ruwan sha mai tsafta a Najeriya saboda karuwar bukatara da ake da ita. Najeriyar dai na cikin yanayi na ga koshi ga kwanan yunwa ne domin tana da albarkatun ruwa mai yawa amma tace shi don amfanin jama'a ya zama matsala. Alal misali akwai matsalar yawan gina rijiyar burtsatse barkatai da ake fama da ita.

Tun da farko Agnes Anieke jami'ar ma'aikatar ruwa da albarkatun kasa ta Najeriya ta bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta bullo da sabbin hanyoyi na zamani domin cimma samar da ruwan sha ga al'umma. Batun matsalar karancin ruwa na haifar da fargaba ta samun wadatar abinci a Najeriyar musamman bisa hasashen da aka yi.

Gwamnatin Najeriya dai tana son samun amincewa da kudurin dokar da ke gaban majalisa wanda zai taimaka sauya tsari da fasalin samar da ruwan sha mai tsafta wanda hakki ne daga cikin hakkokin dan Adam.