An zargi Sojojin Najeriya da cin zarafin jama′a | Siyasa | DW | 01.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An zargi Sojojin Najeriya da cin zarafin jama'a

Ƙungiyar kare hakin jama’a ta ƙasa da ƙasa, Amnesty International ta ce jami'an tsaron Najeriya na ci gaba da tozarta wa Al'umma da sunan yaƙar 'yan ƙungiyar Boko Haram.

Ƙungiyar tace Sojojin na hakan ne a ƙoƙarin murkushe hare-haren da 'yan ƙungiyar Ahlil Sunnah ta Boko Haram ke kaiwa abin da ya haifar da take hakkin jama'a a yanayin da ke nuna kara taɓarɓarewar wannan matsala da ta yi dalilin mutuwar mutane da dama a arewacin Najeriyar.

Rahoton na kungiyar hakin jama'a ta Amnesty Internationa wanda sakamakon kamallaen bincike ne da t ace ta gudanar a Najeriyar day a gano yadda jami'an tsaron ke kasha jama'a ba bisa doka ba, azabtar da jama'a da lalata gidajensu abinda ya nubna zahiri yadda ake ci gaba da take hakin jama'a sakamkon wannan rikici.

Rahoton da ƙungiyar ta yiwa take da Najeriya kasar da tashen-tashen hankali suka yi mata tabaibayi, ya gano irin yadda mutane ke zaune cikin fargabar fuskantar a kai masu hari saboda yadda jami'an tsaron ƙasar ke wuce iyaka wajen murkushe hare-haren da ake kaiwa. Mallam Muhammad Azubair na cikin wadanda suka gudanar da binciken a ƙarƙashin ƙungiyar ta Amnesty International ya bayyana zahirin abin da suka gano.

‘' Mutane sun zo mun gana da fiye da mutum 100 da suka haɗa da mata da yara ƙanana da matan da suka rasa mazajensu da iyaye da suka rasa 'yayansu da kuma waɗanda ake tsare da su. Akwai waɗanda suka shaida mana cewa an ɗaure su a jikin sangalalan fila na siminti sama da sati guda, a lokacin ma da muka gana da su ɗaya daga cikinsu zaka ga shatin da ankwa da ke jikin hannunsa da raunin da ke jikinsu''.

Ƙungiyar ta bukaci gwamnatin Najeriyar ta ɗauki matakan kara jama'a daga wannan mumunan hali da ta zargi jami'an tsaron Najeriyar ke yi a kan farraren hula wacce ked a mumunan illa ga take hakin jama'a. To ko wane kalubale suka hango dangane da wannan rahoto da suka gabatar a yanzu? Mr Shetty Salil sakatren Janar na ƙungiyar ta Amnesty International.

Yace ‘' babban ƙalubalen da muka hango shine mafi yawan waɗannan mutane da aka tsare su ba bisa doka ba, suna a yanayin da basu iya saduwa da kowa kuma ba'a kama su da wani laifi, wannan ya bada kafar gana masu azaba da bacewar wasu, mafi yawan wadannan batutuwa na bukatar bincike cikin hanzari''.

Binciken dai ya bayyana irin munin laifuffukan na take hakin jama'a da ake zargin jami'an tsaron Najeriya a fafatawar da suke yi da yayyan ƙungiyar ta Ahlul Sunna li da'awati wal jihad abinda suka bayyana cewa na kara rusa wutar rigingimu ne. Har ila yau ga Malam Muhammad Zubair wanda ya bayyana munin wannan al'ammari.

‘'Watau wanna ya kai da abin da Bahaushe kan ce halin Lahaula Wala Kuwata domin akwai waɗanda muka tattauna da su wanda zaka ga a kan titi ma yake tafe an tsare shi, ai akwai tsari na doka, amma kawai an kama mutum ana zargin shi dan ƙungiyar Boko Haram ne an tafi da shi an tsare shi ba'a dawo gidanshi an bincika ko da makami ko wani abu, wasu da zarar an kaishu shikenan an manta da su ba wanda zai sake tambayarsu kuma har yanzu dinan da muke Magana akwai wadanda suke tsare''

Koda yake jami'an ƙungiyar ta Amnesty sun bayyana gaza samun uzurin ganawa da shugaban Najeriyar domin gabatar mashi da rahoton amma hakan bai samu ba, to sai dai sun gabatar da rahoton garesu inda mataimakin sifeto janar na mai baiwa shugaban Najeriya shawara a fanin tsaro suka yi alakwarin gudanar da bincike a kan waɗannan zarge-zarge.

Amnesty Internaqtional ta bukaci shugaban Najeriyar da ya fito fili ya yi Allah wadai da dukkanin take hakin jama'a da jami'an tsaron ƙasar ke aikatawa, tare da bayyana sakamakon kwamitocin da suka gudanar da bincike a kan halin tsaro a arewaci da tsakiyar Najeriya.

Wannan rahoto dai ya zo ne a dai dai lokacin da ake kara samun koke-koke na yawaitar kashe jama'a da ake zargin jami'an tsaron Najeriyar na yi a ikirarin da suke na wanzar da zaman lafiya da tsaro musamman a arewa maso gabashin Najeriya, abin da ya sanya wasu kiraye-kiraye lallai sai a janye sojojin saboda kazancewar lamarin.

Jami'an tsaron Najeriyar dai sun daɗe suna musanta wannan zargi da a kullum ke kara da ke nuna yadda yanayin tsaron kasar ke kara shiga mawuyacin hali.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita : Zainab Mohammed Abubakar