An zabi shugaban hukumar Tarayyar Turai | Siyasa | DW | 15.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An zabi shugaban hukumar Tarayyar Turai

Fitaccen dan siyasa a Turai Jean-Claude Juncker, ya bayyana sabbin matakan da zai dauka na farfado da tattalin arzikin kungiyar ta EU

default

Jean-Claude Juncke

Dan shekaru 59 da haihuwa Jean-Claude Juncker, ya samu kuri'u daga duk bangarorin jam'iyyun da ke a majalisar, kama daga bangaren masu sassaucin ra'ayi da kuma 'yan mazan jiya. Sabon shugaban ya bayyana manyan ayyukan da zai sa a gaba cikin wa'adin mulkinsa.

"Zan gabatar da shawarar gagarumin shirin samar da zuba jari. Daga nan zuwa watanni, wannan gagarumin shirin na zaburar da tattalin arziki da kuma ba da damar yin gogayya shi zan gabatar. Ina fatan nan da shekaru uku masu zuwa mu tara Euro biliyan 300."

Tun da farko gabanin zabensa an zaci samun wani gagarunmin sauyi a kungiyar Tarayyar Turai, to amma sabon shugaban hukumar ya ce burinsa shi ne ci gaba da dinkewar Tarayyar Turai. Jean-Claude Juncker ya nuna damuwarsa kan yadda Tarayyar Turai ta samu koma baya bisa wasu al'amura.

Jean-Claude Juncker & Angela Merkel 18.10.2012

Jean-Claude Juncker da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel

Shi dai sabon shugaban hukumar na Tarayyar Turai, shi ne shugaban wata gwamnati da ya fi kowa dadewa yana aiki cikin kungiyar. Tun da ya tsunduma cikin harkokin yake rike mukamai daban-daban da suka hada da ministan kudi, kana daga bisani ya kasance firaministan kasarsa ta haihuwa wato kasar Luxemburg. Daga shekara ta 2005 zuwa shekara ta 2013 Juncker ya kasance shugaban kungiyar kasashen da ke amfani da kudin Euro.

Domin haka ya fuskanci adawa a wannan zaben wajen 'yan majalisar dokoki da ke kyamar Tarayyar Turai musamman wadanda suka fito daga kasar Birtaniya.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Suleiman Babayo

Sauti da bidiyo akan labarin